Dan Gidan Sheik Dahiru Bauchi Ya Ziyarci Sarki Aminu Ado Bayero Tare Da Ba Shi Kyautar Alkyabba Da Carbi.
Sayyadi Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi ya kaiwa Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero ziyara tare da yi masa kyautar Alkyabba da carbi a yammacin yau a fadar shi dake Nasarawa.
A yayin ziyarar yaja hankalin alumar Jihar Kano dasu zauna lafiya su bi doka, yakuma wuce zuwa hubbare domin yiwa Iyaye addua da ke kwance.
Mai Martaba Sarki Alh. Aminu Ado Bayero ya bayyana jin dadin ziyarar girmamawar ya kuma godewa tawagar Sayyadi da kuma aiken gaisuwa ga Sheikh Dahiru Usman Bauchi da addu’ar Allah Ya kara masa lafiya da nisan kwana.
Daga Abdulwahab Sa’id Ahmad