Monday, April 6
Shadow

Kamata yayi ka yi hakuri ka barwa dan kudu ya tsaya takara a 2027>>Wasu ‘yan PDP daga kudu suka gayawa Atiku

Atiku Abubakar 2011 President campaign Photo by www.mortenfauerby.dk ©mortenfauerby 2010 – all rights reserved

Wasu ‘yan PDP daga Kudancin Najeriya sun baiwa Atiku Abubakar bakin cewa ya hakura da maganar tsayawa takara a shekarar 2027 ya barwa dan kudu.

Sun ce ba ma Atiku kadai ba, duk wani dan Arewa kamata yayi ace ya hakura da tsayawa takara a barwa dan kudu ya tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2027.

Kungiyar tace dama can Atiku ne ya fara jawowa jam’iyyar PDP koma baya a shekarar 2014 inda ya jagoranci gwamnoni 5 suka fice daga jam’iyyar suka koma APC suka juyawa Goodluck Jonathan baya.

Shugaban kungiyar, Dennis Shima ne ya fadi haka inda yace ya kamata a bar dan kudu ya kammala shekara 8 kamar yanda Buhari yayi

Karanta Wannan  Budurwarnan da Mawakin Najeriya Burna Boy ya yaudara yayi lalata da ita da sunan zai sai mata motar Lamborghini amma yaki sai mata tace ita yanzu ta siyawa kanta motar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *