Saturday, December 13
Shadow

Ji Yadda ma’aikacin banki ya riƙa naɗar bidiyon tsìraìcìn abokan aikinsa mata a Najeriya, ya nadi Bidiyo 400

Yadda ma’aikacin banki ya riƙa naɗar bidiyon tsiraicin abokan aikinsa mata a Najeriya.

Rundunar ƴansanda a jihar Legas da ke Najeriya ta ce za ta gurfanar da tsophon ma’aikacin bankin Access wanda ake zargi da ɗaukar hotunan tsiraicin abokan aikinsa mata.

Wannan na zuwa ne bayan wata sanarwa da bankin ya fitar a ranar Litinin inda ya bayyana cewa ya miƙa batun zargin ɗaya daga cikin ma’aikatansu a ɓangaren hulɗa da abokan cinikayya, na ɗaukar hotunan tsiraici ga hukumomi.

Sanarwar da suka wallafa a shafin sada zumunta ta ce bankin zai bai wa hukumomi haɗin kai, kuma bankin zai ci gaba da kare mutuncin ma’aikatansa.

Karanta Wannan  Kalli yanda Wata mamakon Gobara da ba'a san daga inda ta taso ba ta barke a kasar Israyla tana ta yaduwa sosai

Bayani da ya fita a makon da ya gabata ya nuna cewa wani ma’aikacin bankin Access ya naɗi bidiyoyin abokan aikinsa mata a cikin ban-ɗaki ba tare da saninsu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *