
Tsohon hadimin shugaban kasa da ya ajiye aikinsa, Hakeem Baba Ahmad ya bayyana daya daga cikin matsalolin da ya fuskanta a fadar shugaban kasar.
Yace babbar matsala da suka fuskanta itace basa samun ganin Shugaban kasa a matsayinsu na wanda suke masa aiki kuma suna cikin fadar.
Yace shugaban kasar baya samun bayanai na gaskiya akan halin da talakawa ke ciki.
Yace a watanni 18 da yayi a fadar shugaban kasar, sau 3 kacal ya taba haduwa da shugaban kasar shima kuma a masallaci ne.