Majalisar Jihar Kaduna ta bayyana cewa a lokacin Malam Nasiru Ahmad El-Rufai yana mulkin jihar, an cire Naira Biliyan 423 ba tare an yi wani aiki da kudin ba daga asusun gwamnatin jihar.
Hakanan kuma an cire wata Biliyan 30 daga ofishin Kwamishinan kudi da babban akanta na jihar.
Jimulla, an cire Tiriliyan 1.4 daga asusun gwamnatin jihar Kaduna.
Hakan ya bayyana ne daga bakin dan majalisar jihar ta kaduna, Henry Mara wanda shine me magana da yawun Majalisar a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV.