A jiyane dai muka samu rahoton cewa, kasar Israela ta kai wani mummunan hari a garin Aleppo dake kasar Syria wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane da yawa ciki hadda me baiwa kasar Iran shawara akan harkar soji.
A martanin kasar Iran kan harin, Kwamandan dakarun IRGC na kasar Salami ya bayyana cewa, Israela ta saurari harin ramuwar gayya.
A baya dai, irin wannan harin ne Israela ta kai kan ginin ofishin jakadancin Iran wanda ya kashe wasu janarorin soja na Iran.
Hakan yayi sanadiyyar harin ramuwar gayya akan Israela da Iran ta yi wanda ya baiwa Duniya mamaki kuma ya tayar da hankalin kasar Israela.
A wannan karin dai ba’a san wane irin harin ramuwar gayyane Iran zata kai akan Israela ba.