Friday, December 12
Shadow

Gwamnan Katsina ya ba da hutun aiki saboda ziyarar Tinubu

Gwamnan jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ya ayyana yau Juma’a a matsayin ranar hutu ga ma’aikata domin “tarɓar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu” da ke ziyara a jihar tasu.

Gwamna Dikko Radda ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin jawabin da ya gabatar a taron Ranar Ma’aikata.

“Ina mai farin cikin shaida muku cewa Shugaba Tinubu zai kawo ziyara Katsina gobe [Juma’a] domin buɗe ayyuka da dama da muka kammala cikin shekara biyu da suka wuce,” in ji gwamnan.

“Saboda haka, na ayyana goben a matsayin ranar hutu saboda ma’aikata su samu damar haɗuwa da mu wajen tarɓar shugaban ƙasa.”

A jiya Alhamis ne fadar shugaban Najeriya ta sanar cewa Tinubu na jam’iyyar APC zai kai ziyarar aiki ta kwana biyu a jihar da ke arewa maso yamma kuma ta tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

Karanta Wannan  Babban Lauya, Femi Falana ya shigar da bukatar sakin yaran da aka kama da kuma basu ilimi kyauta, Sannan yace kotun ma bata da hurumin yi musu Shari'a

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *