Wannan matar an kamata da harsasai 2000 zata kaiwa ‘yan Bindiga a jihar Zamfara.
Jami’an tsaron sun kamata ne da makaman amma babu cikakken bayanan me ya faru.
Hakanan wasu ‘yan Boko Haram, Baana Duguri, Momodu Fantami, Abubakar Isani da Zainami Dauda sun mika kansu wajan jami’n tsaro inda suka ce sun tuba.
An kwace makaman Bindigar Ak47 guda 2, da Harsasai masu yawa, da wasu kananan bamabamai da mashina 2, da dai sauransu.
Sun bayyana cewa, sun fito ne daga garin Damboa.