
Shugaba Tinubu Ya Ƙaddamar Da Sabbin Jiragen Yaƙi Masu Saukar Angulu Samfurin Agusta A-109Power Attack
A wani ɓangare na kokarin sabunta tsarin tsaron ƙasa. Shugaba Tinubu ya wakilta mataimakinsa Kashim Shettima wajen kaddamar da Sabbin jiragen yaƙin
Shettima ya jaddada kudirin gwamnatin Najeriya na shiga dumu-dumu hannun cikin harkar inganta sabbin fasahohin aiyukan tsaron ƙasa domin wadata sojojin Najeriya da abubuwan da suka dace don tunkarar kalubalen tsaro.
Gwamnatin ta kuma tabbatar wa da hukumar sojojin saman Najeriya ta NAF da cewa za ta sami ƙarin jiragen yaƙi sama 49 a cikin shekaru biyu masu zuwa.
Shugaban ya kuma bukaci sojojin saman da su kiyaye ɗa’a da bin ƙa’idojin aiki don cin gajiyar manufofin aiki