
Gwamnatin jihar Bauchi ta tallafawa tubabbun mata karuwai da masu shaye-shaye da suka daina da kayan sana’a dan dogaro da kai.
An tattaro matanne daga karamar hukumar Misau ta jihar ta Bauchi wanda ke karuwanci da shaye-shaye inda aka tallafa musu a karkashin tsarin Better Life Restoration Initiative (BERI).
Daya daga cikin matan da suka amfana da wannan lamari ta bayyana cewa ta samu canjin rayuwa a yanzu an bata sana’a amma tace matsalar daya ce shine har yanzu ana hantararsu.