Friday, December 5
Shadow

Arewa maso yamma ta Tinubu ce a 2027>>Inji APC

APC a shiyyar Arewa-maso-yamma ta sanar da goyon bayan ta ga Tinubu a zaɓen 2027.

Jam’iyyar APC a shiyyar Arewa-maso-yamma ta kada kuri’ar amincewa da shugaba Bola Tinubu a matsayin dan takara gabanin zaben shugaban kasa na 2027.

An bayar da amincewar ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Kaduna a jiya Asabar, inda kuma aka amince da Tinubu a matsayin dan takarar daya tilo.

A cikin sanarwar da Uba Sani, gwamnan jihar Kaduna ya karanta, shiyyar ta jaddada biyayyar ta ga jam’iyyar APC tare da yin alkawarin “cikakken goyon baya ga manufar shugaba Tinubu na samar da wadata, daidaito da kuma sauyi mai dorewa ga daukacin ‘yan Najeriya”.

Karanta Wannan  Burin kowane Tshàgyèràn Dhàjì dake kasashen Afrika shine ya zo Najeriya saboda a tunaninsu Najeriya akwai kudi>>Inji Janar Christopher Musa

“Muna godewa kuma muna yaba wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa kyakkyawan jagoranci da ya ke yi, da sauye-sauyen da ya yi, da kuma jajircewarsa na ci gaban Nijeriya, musamman a shiyyar Arewa maso Yamma,” in ji sanarwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *