
Karamin yaro dan shekaru 16 ya dauki Bindigar mahaifinsa ya harbe kanwarsa ta mutu har lahira a jihar Delta.
Kakakin ‘yansandan jihar, Bright Edafe ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace lamarin akwai sosa Zuciya.
Ya kara da cewa, mahaifin yace shi mafarauci ne kuma dan nasa yakan rika wasa da Bindigar.
Yace zuwa ya zu ba’a kai ga tantance sunayen wadanda lamarin ya faru dasu ba.