Daliba ‘Yar Shekara 15 Ta Zama Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina Na Wucin-Gadi Na Tsawon Mintuna Biyar

Daga Comr Nura Siniya
Shugaban majalisar dokokin jihar Katsina Hon. Nasiru Yahaya Daura, ya miƙa ragamar shugabancin majalisa na minti 5 ga wata ɗaliba mai hazaƙa Marwa Nasir Yahaya, a lokacin da daliban makarantar suka kawo ziyarar duba ayyukan majalisar, domin sanin makamar aiki, a ranar Litinin 19 ga watan Mayu 2025.
Katsina Reporters ta samu cewa, daliban makarantar “Little Angel ne suka zaɓi Marwa Nasir Yahaya, saboda kwazonta ga harkar ilimin addini da na zamani.
Ɗalibar dai ta kasance ɗiya ga shugaban majalisar dokokin na jihar Katsina.