
Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah ya baiwa dan Arewa,Alhaji Abubakar Yusuf Sambo mukamin me bashi shawara akan ayyuka na musamman.
Alhaji Abubakar Yusuf Sambo dai kuma shine sarkin Hausawan Enugu.
A Enugu aka haifeshi kuma yana jin Inyamuranci sosai.
Hakanan Gwamnan jihar Enugu ya bashi mukamin mem ba na kwamitin tsaro na jihar.