
Wani kwamandan Boko Haram da ya kira kansa da cewa shi ne sabon “Shekau,” ya yi barazana ga babban hafsan hafsoshin Najeriya, CDS, Christopher Musa, da malaman addinin Musulunci, da jami’an tsaro, da kuma al’ummomin da ke goyon bayan ayyukan gwamnati na yaki da ta’addanci.
Barazanar ɗan ta’addan ba ta rasa nasaba ga gargadin da Musa ya yi tun farko a cikin harshen Hausa, inda ya yi kira ga yan ta’addan da su mika wuya ko kuma su fuskanci fushin sojojin Najeriya.
A wani sabon faifan bidiyo da kafar yada labarai ta PRNigeria ta samu kuma ta fassara daga Hausa zuwa turanci, maharin ya mika sakon ban tsoro ga Janar Musa, inda ya bukaci shi da rundunar sojojin Najeriya da su yi watsi da yakin da suke yi da kungiyar.
Ya yi ikirarin cewa, kamar magabatan sa, Musa ba zai yi nasarar murkushe Boko Haram ba.
“Wannan sakon na babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ne, muna kira gare ka da ka tuba ka daina ayyukan da kake yi, domin ba za ka yi nasara a kan wadanda mu ke yaki da gwamnatinka ba,” in ji ɗan tawayen.