Friday, December 5
Shadow

Jimullar masu laifi 2000 ne suka tsere daga gidajen yarin Najeriya kuma ake nema ruwa a jallo

Bayan tserewar masu laifi daga gidan yarin Ilesa na jihar Osun su 7 ranar Talata, an gano cewa akwai masu laifi 2000 da suka tsere daga gidajen yari daban-daban na Najeriya da ake nema ruwa a jallo.

Haka na zuwane wata daya kacal bayan da masu laifi 12 daga gidan yari me suna Katon Karfe suka tsere daga jihar Kogi.

A shekarar 2024 ma dai an samu tserewar masu laifi daga gidan yarin MCC dake Suleja jihar Naija inda masu laifi 118 suka tsere amma guda 23 ne kawai aka samu damar sake kamowa.

Hakan na zuwane yayin da laifuka da kashe-kashen da ayyukan ta’addanci suka yi yawa a Najeriya.

Karanta Wannan  Maganar canja tsarin karatun Najeriya daga JSS da SSS zuwa shekaru 12 ba gaskiya bane>>Inji Gwamnatin Tarayya

Rahoton yace zuwa yanzu akwai jimullar masu laifi 2000 da suka tsere daga gidajen yarin Najeriya daban-daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *