
Dan siyasar jihar Ekiti wanda kuma dan uwa ne ga tsohon gwamnan jihar, Isaac Fayose ya caccaki mutanen jiharsa.
Ya bayyana su da marasa wayau inda yace ana basu kudi kalilan suna zaben gurbatattun ‘yan siyasa.
Yace bayan zabe haka zaka ga sun koma mabarata.
Maganar tashi ta jawo cece-kuce sosai inda mutanen jihar suka bayyana rashin jin dadinsu, saidai yace shi har yanzu yana nan kan bakarsa.