
Ana Gudanar Da Taron Haɗaka Tsakanin Manya ‘Yan Siyasar Jam’iyyun Hamayya A Nijeriya.
A wajen taron an hango Tsohon Mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa Peter Obi, shugaban BOT na PDP, Adolphus Wabara, da sauran manyan ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki.
An yiwa taron laƙabi da (National Political Consultative Group (North) .
Ana sa ran tattaunawa kan makomar siyasar Arewa da haɗa ƙarfi don fuskantar manyan zaɓuka masu zuwa a 2027.
Me zaku ce?