
Rahotanni daga Kano sun ce fada da ya barke tsakanin matasan kauyukan Faruruwa dana Tarandai dake karamar hukumar Takai ta jihar yasa an yi asarar rai.
Lamarin ya farune a kasuwar garin Faruruwa ranar 23 ga watan Mayu da misalin karfe 7:45 p.m.
An yi fadanne ranar Kasuwar garin inda aka kona runfunan Kasuwa da dama.
Rahoton yace wani me suna Sani Yunusa, 28 daga kauyen Toho Diribo dake karamar hukumar Takai ya je wajan budurwarsa dake kauyen Tarandai.
Saidai matasa sun afka masa da duka da itace.
Tuni aka aika da jami’an tsaro yankin dan su kwantar da tarzomar.
Rahoton yace ana kokarin kama wadanda suka fara tada tarzomar dan yi musu hukunci.