
Rahotanni sun bayyana cewa Jimullar Naira Tiriliyan 7 ne gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta samu bayan cire tallafin Man fetur.
Saidai duk da haka, talakan Najeriya bai shaida ba inda ake ci gaba da fama da tsadar rayuwa da Talauci da matsalar tsaro.
Wadannan karin kudade da aka samu an karawa gwamnatoci a kowane mataki watau Tarayya, jiha da kananan hukumomi yawan kudaden da suke samu.
Sannan an sayo motoci masu amfani da Gas me Arha sannan an rabawa talakawa kudaden Tallafi sannan an kashe makudan kudade wajan gyaran matatun man fetur din da muke dasu amma duk da haka babu Alamar shaida hakan ga Talaka.
Yawanci kasuwanci da kamfanoni musamman kanana da matsakaita sun rage ma’aikata wasu ma sun kulle inda Bankin Duniya, da IMF ke kara tabbatar da cewa akwai mutane da yawa masu fama da Talauci a Najeriya.