
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, ‘yan Bindiga ne ke mulkar Najeriya.
El-Rufai yace dan haka Najeriya na cikin tsaka mai wuya.
El-Rufai yace ‘yan Najeriya na ci gaba da maimaita kuskuren da suka yi a baya na zabar shuwagabannin da bana gari ba.
Ya bayyana hakane a babban birnin tarayya, Abuja ranar Asabar a wajan wani taro.
Yace Najeriya na cikin matsalar da bata taba shiga ba tun shekarar 1914 a yayin sa aka hade Arewa da kudu.
Yace mafi yawancin shuwagabannin basu san yanda zasu gudanar da mulki ba kawai su dai su samu mulkin shine a gabansu.