Monday, April 6
Shadow

Ji mugun abin da wannan dansandan yayi da ake ta murna bayan mutuwarsa

Da yawan mutane na ta murna da mutuwar dansanda me suna CSP Ekene Nwosu dake aiki a jihar Akwa-Ibom.

Kamin mutuwarsa, shine ke kula da bangaren yaki da ‘yan fashi na hukumar ‘Yansandan jihar.

Saidai da yawa sun bayyanashi a matsayin mugu wanda ya zalunci mutane da dama a yayin gudanar da aikinsa.

Wani babban lauya me suna Inibehe Effiong ya bayyana marigayin a matsayin mugu wanda ‘yan siyasa ke amfani dashi suna cimma burinsh.

Yace abin mamaki ne ganin yanda aka barshi ya ci gaba da aiki a matsayin dansanda duk da irin bakin halinsa.

Saidai yace yana fatan mutuwarsa zata zama izina ga sauran ‘yansanda masu hali irin nasa.

Karanta Wannan  Kalli Hotuna: An kama Wasu Kiristoci, ciki hadda ma'aikacin coci da Daukar dan 'yan uwansu dan a basu kudin Fwansa

Ba wannan lauyan ne kadai yayi korafi akan dansandan ba da yawa sun bayyana cewa bashi da kirki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *