
Tsohon Ministan Muhalli a zamanin Mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, watau Mohammed Abdullahi ya bar jam’iyyar APC.
A karkashin Mulkin Buhari an nada Muhammad Abdullahi a matsayin karamin Ministan Kimiyya da Fasaha kamin daga baya aka mayar dashi ministan Muhalli.
Ya bayyana barin jam’iyyar APC ne a wasikar da ya aikewa jam’iyyar reshen mazabar sa dake Uke ward karamar hukumar Karu, Jihar Nasarawa.
Ya bayyana dalilai na kashin kansa ne suka sa ya bar jam’iyyar inda yace ya gode da damar da aka bashi ta gina jam’iyyar tare dashi.
A baya kamin ya zama Ministan, ya rike mukamai da yawa a jihar Nasarawa ciki hadda babban sakataren gwamnati da Kwamishina.