
Ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, wanda ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya, ya taya daukacin al’ummar musulmi na gida da kuma na kasashen waje murnar sallah.
Ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su ci gaba da yin koyi da sadaukarwa da imani da kuma amfani da wannan lokacin wajen yi wa Nijeriya addu’a ta zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ministan ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa gyare-gyare da tsare-tsare da suka shafi jama’a da aka yi, a ci gaban ajandar sabunta fata na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, shi ne dawo da Nijeriya kan turbar ci gaba.
Yayin da yake yiwa al’ummar musulmi barka da Sallah, Ministan ya bukaci dukkan ‘yan Najeriya da su hada kai da gwamnati mai ci a kokarinta na dawo da martabar Najeriya a matsayin kasa mai girma.