Friday, December 5
Shadow

Mahaifiyar dalibi me rubuta jarabawar WAEC ta dauko hayar ‘yan Iska sun zane malamin danta saboda ya hana dan nata satar Jarabawa

Wani malami a makarantar Complete Child Development College Aule dake Akure jihar Ondo ya sha duka bayan da ya hana daya daga cikin dalibansa satar jarabawa a yayin da ake rubuta jarabawar WAEC.

Ana zargin mahaifiyar dalibinne ta dauki hayar ‘yan Iska suka zane malamin

Dama dai malamin da farko ya hana dalibin satar jarabawa saidai dalibin yaki dainawa inda ya gayawa mahaifiyarsa.

Mahaifiyarsa ta je makarantar inda ta yi barazanar yin maganin duk wanda ya sake ya hana danta satar Jarabawa.

Saidai malamin me suna Rotifa wanda shine mataimakin shugaban makarantar ya sha alwashin sai ya hana dalibin satar jarabawar duk da barazanar mahaifiyarsa.

Karanta Wannan  Amarya, Rahama Sadau ta godewa 'yan Uwa da abokan arziki da suka tayata Biki

Hakan kuwa aka yi da dalibin ya koma makarantar sai ya je da waya ya fiddo zai yi satar Amsa amma malamin ya kwace wayar.

Nan ne mahaifiyar dalibin ta dauko ‘yan iska suka zane malamin har sai da aka kaishi Asibiti.

Gwamnatin jihar Ondo ta sha Alwashin yin maganin lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *