Gwamnatin jihar Neja ta soke hawan sallah sakamakon ambaliyyar ruwa a Mokwa.

Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago, ya bada umarnin soke bukukuwan babbar sallah tare da dakatar da Hawan Bariki, da sauran bukukuwan Sallah a dukkan masarautun jihar.
Umurnin ya biyo bayan mummunan ibtila’in ambaliyar ruwa da ta yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi a garin Mokwa da kewaye.
Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Abubakar Usman a lokacin da ya ke sanar da wannan umarni, ya ce an dauki matakin ne a matsayin girmamawa ga wadanda lamarin ya rutsa da su da kuma ba da damar zaman makoki da addu’o’i.
Da ya ke mika umarnin Gwamnan ga Masarautu, Sakataren Gwamnatin ya bayyana cewa, ambaliyar Mokwa na daya daga cikin mafi muni da aka yi a jihar tsawon shekaru da dama da suka gabata, kuma ya yi sanadin salwantar rayuka da rugujewar gidaje da ababen more rayuwa.