
Wata matashiya ta dauki hankula a kafafen sada zumunta bayan da tace idan mutum bashi da Miliyan 50 ba zata iya aurensa ba.
Ta bayyana hakane a wani shirin da ake hira da ita.
Tace miliyan 50 din da take magana ba wai na wani abu bane, na shagalin bikine take magana akai.
Da yawa dai sun bayyana mamaki da wannan ikirari nata.