
Rahotanni da muke samu na cewa, tawagar motocin tsohon shugaban sojojin Najeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai ta tsallake rijiya da baya bayan da ‘yan Bindiga suka bude mai wuta.
Hutudole ya samo cewa, Lamarin ya farune ranar Juma’a watau Ranar babbar Sallah data gabata a jiharsa ta Borno.
Ana zargin, Kungiyar mas ikirarin Jìhàdì ta Bòkò Hàràm ce ta kai harin wanda hakan ke kara nuna irin yanda kungiyar ta dawo da karfinta a ‘yan Kwanakinnan.
Sanata Ali Ndume da ya fito daga jihar ne ya bayyana haka a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV ranar Lahadi.
Yace ‘yan Bòkò Hàràm din sun afkawa tawagar Buratai ne da harin kwantan bauna inda suka lalata motoci da dama suka kwashi makamai duk da yake cewa sojojin dake tare da Buratai din sun mayar da martani.