Monday, December 16
Shadow

Masu zanga-zanga sun yi artabu da ƴan sandan Isra’ila

Masu zanga-zangar ƙin jinin gwamnati sun yi taho mu gama da ƴan sanda, a daidai lokacin da ake gangamin a sassan Isra’ila kan kiran a kuɓutar da sauran waɗanda ke hannun Hamas.

Sai dai mai magana da yawun sojin ƙasar,Rear admiral Daniel Hagari ya ce su na ƙoƙari kan batun.

Ya ce dakarun Isra’ila sun ɗauki makwanni su na shirye-shiryen aikin nan, an ba su horo kan yadda za su kuɓutar da mutanenmu, ba za mu gaji ba har sai sauran sun dawo.

Masu zanga-zangar su na sukar firaiminista Benjamin Netanyahu, wanda ke ganawa da iyalan waɗanda aka saka maimakon waɗanda ke cikin tashin hankali da rashin tabbacin ko nasu ƴan uwan za su dawo gida a raye.

Karanta Wannan  A yaune Ministan kudi zai gabatar wa da shugaba Tinubu sabon daftarin mafi karancin Albashi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *