
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, sai da ya gargadi duka manyan sojojin Kasar Ìràn cewa a yi sulhu amma suka kiya.
Yacw gashinan duk an kashesu.
Yace Ya gargadesu Amurka ce ke kera makaman da babu irin su a Duk Duniya, kuma kasar Israyla na da wadannan makamai kuma ta iya aiki dasu.
Yace amma duk suka ki saurarensa.
Yace amma har yanzu akwai sauran lokaci be kure ba, kamin a gama lalata kasar Iran din baki daya, zasu iya zuwa a yi sulhu.
A ranar Alhamis ne dai ake sa ran ci gaba da tattaunawar sulhu tsakanin Amurka da Iran kan shirinta na mallakar makamin kare dangi.
Saidai Iran din tace ba zata halarci ci gaba da tattaunawar ba.