Friday, December 5
Shadow

Hare-haren da ake kaiwa jihar Benue sun kai matakin da ba zamu kauda kai ba>>Atiku Abubakar

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar yayi Allah wadai da hare-haren da aka kai jijar Benue.

Atiku yace hare-haren sun kai matakin da ba za’a iya kauda kai ba.

Yace wani abin takaici shine yanda ake harbawa masu zanga-zangar da suka fito suke nuna damuwa kan lamarin barkonin tsohuwa.

Yace suna neman a basu tsaron rayuwarsu ne.

Yace yana kira ga hukumomi su daina yin Allah wadai kawai su rika tashi tsaye suna daukar mataki.

Yace kuma ba jihar Benue bace kadai akwai jihohin Zamfara, Katsina, Plateau, da Taraba dake fama da irin wannan matsala ta tsaro.

Karanta Wannan  Hotuna:Kalli Yanda 'yan Najeriya dake kasar Ingila suka fara zàngà-zàngà

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *