
Gwamnatin jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce za ta soma shirin sauya tunanin tubabbun ƴanbindigar da suka miƙa makamai nan bada jimawa ba.
Gwamnatin ta ce za a buɗe azuzuwan koyar da karatu da dubarun koyar da sana’o’i domin sauya tunanin ƴanbindigar, inda daga bisani za su koma cikin al’umma.
Hukumar da ke kula da ilimin manya ta jihar ce ke da alhakin tsara yadda shirin sauya tunanin tubabbun ƴanbindigar zai kasance.
Ƙarƙashin shirin za a bai wa waɗanda suka miƙa makamansu damar koyon karatun zamani da na addinin musulunci tare da fahimtar da su illar kisan mutane da kuma neman fansa.
Daraktar hukumar ilimin manya ta jihar Katsinan Bilkisu Muhammad Kakai, ta tabbatarwa da BBC wannan shiri da gwamnatin jihar zata fara.
Daraktar ta sanar da manema labarai cewa nan bada jimawa ba za a tura waɗanda za su fara bayar da aikin horon zuwa ƙananan hukumomin jihar don fara horar da tubabbun ƴan bindigar.
To sai dai kuma duk da wannan yunƙuri na gwamnatin jihar, masana lamuran tsaro na ganin da wuya a samu nasarar ɗorewar shirin muddin ba kula da waɗanda hare-haren da ƴan bindigar suka shafa ba.
Barista Audu Bulama Bukarti, mai bincike ne a kan al’muran tsaro a nahiyar Afirka ya shaida wa BBC cewa, dole ne gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da cewa ta ɗauki matakan tabbatar da cewa ungulu bata koma gidanta na tsamiya ba.
Ya ce,” Kamar a baya na gani a arewa maso yammacin Najeriya inda wasu ƴan bindiga da aka yi yarjejeniya da su kan sun tuba amma daga bisani suka koma ruwa.”
” Mun ga yadda gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce akwai wasu ƴan ƙungiyar Boko Haram da suka tuba har ma an wanke musu kwakwalwa to amma sai aka ga wasu daga cikinsu sun koma ruwa.”
Barista Bulama Bukarti, ya ce,” Ya kamata a rinka waiwaye ana duba irin al’ummar da waɗannan tubabbu suka cutar domin samar musu da rayuwa mai inganci a yayin da ake shirin sauya tunanin su ƴan bindigar domin idan har ba a yi haka ba to da wuya zaman lafiya ya ɗore domin su mutanen da ƴan bindigar suka cutar za su ga kamar ana goyawa waɗanda suka cutar da su baya ne.”
Jihar Katsina dai na daga cikin jerin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da hare-haren ƴan fashin daji, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a jihar.