Monday, February 9
Shadow

Gwamnatin tarayya ta kwace mukamin Jakadancin data baiwa Usman Nasamu Dakin Gari

A daren jiyane dai gwamnatin tarayya ta bayyana Usman Nasamu Dakin gari a matsayin jakadan Najeriya a kasar Turkiyya.

Saidai a yau da Safiyar Juma’a, Gwamnatin ta bayyana kwace wannan mukami.

Zuwa yanzu dai ba’a bayyana dalilin Gwamnatin na kwace wannan mukami ba.

Duka sanarwar nadashi da kwace mukamin ta fito ne daga bakin me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga.

Ana tsammanin nan ba da jimawa ba, shugaba Tinubu zai kai ziyara kasar ta Turkiyya.

Karanta Wannan  Sarkin Kano Khaleefa Muhammad Sanusi II, ya ziyarci Tsohon Shugaban Kasar mulkin soja Nigeria a Birnin London

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *