Rahotanni sun bayyana cewa kananan matatun man fetur na cikin gida ka iya karya farashin man fetur.
Ana sa ran idan matatar man fetur ta Dangote da sauran matatun man fetur kanana suka fara aiki hakan zai sa farashin man fetur din ya karyo kasa.
Saidai masana sunce idan ana son hakan ya tabbata watau farashin litar man fetur din ya dawo Naira 300 sai gwamnati ta tabbatar da ana baiwa matatun man na cikin gida isashshen danyen man fetur.
A baya dai mun ji yanda Aliko Dangote ya koka da cewa, matatar mansa bata iya sayen danyen man Najeriya saboda kamfanonin dake hako man a cikin gida sun fi son su kai kasashen waje su sayar da danyen man fetur din.