Rahotanni sun bayyana cewa, an yi garkuwa da mutane 25 da kuma wasu dalibai akan hanyar Abuja zuwa Nasarawa.
Lamarin ya farune ranar Juma’a kamar yanda jaridar Punch ta ruwaito kuma yawan wadanda aka yi garkuwa dasu sun kai 30.
Direban motar dai ya kubuta inda ya kaiwa ‘yansanda rahoton faruwar lamarin.
Hukumar ‘yansanda ta jihar Nasarawa ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakinta,Rahman Nansel inda tace an kubutar da mutane 3 daga cikin wadanda aka yi garkuwa dasu kuma ana kan kokarin kubutar da sauran.