
Malaman Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta jihar Kaduna watau Nuhu Bamalli Polytechnic, Zaria sun koka da karancin Albashi inda suka ce matasa masu bautar kasa sun fi su daukar albashi me kyau.
Hakanan malaman Kwalejin ilimi ta jihar, College of Education, Gidan Waya suma sun koka akan irin wannan lamari.
Jaridar Punchng ta ruwaito cewa, malaman Makarantar na daukar albashin 63,000 zuwa 65,000. A yayin da su kuma matasa masu bautar kasa ake biyansu Naira 77,000 duk wata.
Malam sun ce wannan cin fuska ne kuma ta yaya mutum mai iyali zai iya gudanar da rayuwarsa da Albashin Naira 65,000 a wata?
Rahoton yace malaman zun zargi cewa hakan nuna halin ko in kula ne a bangaren ili a jihar, wasu daga cikin malaman dai na da kwarewa ta shekaru 10.
Rahoton yace wannan dalili yasa malamai sun fara ajiye aikin koyarwar.