Friday, December 5
Shadow

Yanzu-Yanzu: Otal din da sabuwar jam’iyyar su Atiku, ADC ta kama dan yin amfani dashi wajan yin bikin shiga aabuwar jam’iyyar yace taron ba zai yiyu ba, ana zargin APC da hannu a lamarin

Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja na cewa, Otal da su Atiku suka kama dan yin bikin komawa sabuwar jam’iyyar ADC ya gaya musu cewa taron ba zai yiyu ba.

Su Atiku sun shirya yin taronne a ranar Laraba dan tabbatar da komawa jam’iyyar ADC, saidai awanni kamin taron, Otal din yace musu taron ba zai yiyuba.

Otal din me suna, Wells Carlton Hotel and Apartments a sanarwar da ya fitar yace umarnine daga sama aka basu.

Shahararren dan jarida, Dele Momodu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Ana dai zargin jam’iyyar APC na da hannu a lamarin.

Saidai hadakar ta su Atiku tace wannan ba zai hanata cimma burinta ba.

Karanta Wannan  Na cikawa Al'ummar Kano yawancin Alkawuran dana musu>>Gwamna Abba Gida-Gida

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *