
A jiyane dai aka yi babban taro na hadakar ‘yan adawa da suka bayyana jam’iyyar ADC a matsayin wadda zasu koma cikinta.
Ga jadawalin sunayen manyan ‘yan Adawar da suka koma jam’iyyar ta ADC ko wanda suka halarci taron na jiya.
Akwai Atiku Abubakar; Peter Obi; Da Rauf Aregbesola.
Victor Umeh wanda shugaban jam’iyyar APGA ne sai tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Prince Uche Secondus, Mataimakin Peter Obi, Datti Baba-Ahmed.
Tsohon shugaban jam’iyyar APC John Odigie-Oyegun, tsohon shugaban ‘yansandan Najeriya, Mohammed Abubakar.
Tsaffin Gwamnoni a waja taron sun hada da Nasir El-Rufai (Kaduna), Rotimi Amaechi (Rivers), Gabriel Suswam (Benue), Abdulfattah Ahmed (Kwara), Aminu Waziri Tambuwal (Sokoto), Oserheimen Osunbor (Edo), Celestine Omehia (Rivers), Liyel Imoke (Cross River), Window Jibrilla (Adamawa), Emeka Ihedioha (Imo), Capt. Idris Wada (Kogi).
Akwai kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar Ondo, Agboola Ajayi, tsohon mataimakin Gwamnan jihar Ekiti, Kolapo Olushola, da tsohon mataimakin gwamnan jihar Kogi, Simon Achuba
Akwai tsohon Ministan shari’a, Abubakar Malami, akwai tsohon sakataren Gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, da Senator Dino Melaye.
Da tsohon Ministan matasa, Solomon Dalung, da Babban dan Jarida, Dele Momodu, akwai kuma Senators Enyinnaya Abaribe, Suleiman Nazif, Lee Maeba, Alhaji Kashim Imam.
Akwai tsohon shugaban sojojin saman Najeriya, Air Marshal Sadique Baba Abubakar, da Senator Ishaku Abbo.
Tsohon mataimakin shugaban APC na arewa maso yamma, Salihu Salihu Lukman da kuma sanata dake wakiltar babban birnin tarayya, Abuja, Ireti Kingibe da ‘yar Gwagwarmaya, A’isha Yesufu.