
Wata kungiya me suna, Nigeria Patriotic Front Movement (NPFM) na shirya zanga-zanga nan da 1 ga watan Augusta saboda matsin tattalin arziki, tsadar rayuwa da sauransu.
Kungiyar tace taken zang-zangarta shine babu abinci, babu aiki, babu tabbas a rayuwa.
Kungiyar tace zata tara matasa a manyan garuruwan Najeriya dan yin zanga-zangar da neman kawo karshen mulkij rashin adalci wanda tace ya jefa mutane da yawa cikin Talauci.
Kungiyar dai Tuni ta fara raba takardun yayata zanga-zangar tata a tsakanin al’umma.