
Tsohon Gwamnan jihar Nasarawa, Tanko Almakura ya bayyana cewa, shi rakumi da akala ne a hannun shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Hakan na zuwane a yayin da ake kiran shugaban kasar ya baiwa Tanko Almakura shugaban jam’iyyar APC.
Hakan na zuwane bayan da tsohon shugaban jam’iyyar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sauka daga shugabancin jam’iyyar.
Almakura da aka tambayeshi ko zai amince da mukamin, yace shi a halin yanzu, duk abinda shugaban kasa yace yayi, zai yi.
Yace idan shugaban kasa yace ya je ya rika goge masa Teburinsa, yace da gudu zai rika zuwa yana yi ba haufi.