
A karin Farko tun bayan da ya sayi Motar G-Wagon wadda yace ta fi ta Dauda Kahutu Rarara tsada sannan zata sayi ta Rarara nunki 3 hadda canji, Nazir Ahmad Sarkin Waka ya fito yawo da sabuwar motar tasa.
An ga Naziru yana tuka motar tasa ana masa shewa da barka.
Sannan kuma an ga yanda ya je wajan wani taro da motar ana ta rubibin Kallonsa:
Bidiyon Naziru da wasu suka bayyana cewa na Fariya ne ya jawo cece-kuce sosai a kafafen sada zumunta.