
Wani Bidiyon ziyarar da Peter Obi ya kawo Arewa ya dauki hankula.
An ga Peter Obi a tsakiyar malamai irin su Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun da sauransu.
A yayin da Sheikh Abubakar Salihu Zariya kewa Peter Obi Addu’a yayi Addu’ar cewa, idan Peter Obi ba Alheri bane ga Najeriya, Allah ya kasheshi kamin zabe.
Da yake da Hausa yake addu’ar, da yawa sun ce Peter Obi bai san abinda malam ke cewa ba, wasu kuma abin dariya ya basu.