Friday, December 5
Shadow

Ji bayani dalla-dalla game da kamun da jami’an tsaro sukawa Dan Bello

Yadda aka kama Ɗan Bello tare da sakin sa a filin jirgin sama na Kano.

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[“local”],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Jami’an tsaro sun kama shahararren ɗan gwagwarmayar shugabanci na gaskiya a kafafen sada zumunta, Bello Habib Galadanci, wanda aka fi sani da Dan Bello, bayan isowarsa Nijeriya a yau Asabar a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano (MAKIA) da ke Kano.

Ganau sun ce wani rukuni na jami’an tsaro ne su ka yi wa Dan Bello tara-tara sannan su ka tafi da shi.

LEADERSHIP ta rawaito cewa sai dai bayan ƴan mintuna a tsare, sai aka sako Dan Bello, wanda ke zaune a kasar China, kuma kwai yanzu babu wani bayani da hukumomin tsaro kan dalilin kama shi.

Karanta Wannan  'Yan Bindiga sun kai hari a Matazu, jihar Katsina ana tsaka da sallar Isha'i

Daga bisani, wani lauya sananne kuma aboki na kusa ga Dan Bello, Abba Hikima, ya saka hotonsa tare da Dan Bello a shafinsa na Facebook da rubutun “Guys, we’re good!” wanda ke nuni da cewa an sako shi.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Dan Bello ya yi shura wajen fallasa aiyukan badakala da almundahana da masu riƙe da madafun iko ke yi a Nijeriya.

An Kama Dan Bello A Kano

Wasu rahotanni daga filin jirgin sama na Malam Aminu Kano na bayyana cewar jami’an tsaro da ake zargin daga Abuja suke sun kama matashi nan Bello Habib Galadanci da aka fi sani da Dan Bello.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Dangote zai sayar da wani sashe na matatar mansa

Karin Bayani:

Daga Karshe Dai An Saki Dan Bello Bayan ‘Yan Mintuna Kadan Da Kama Shi.

Karin Bayani:

Duk Da Cewa Wasu Rahotanni Sun Nuna Cewà Ta Kàrfìn Tšìyà Jamì’an Tsaŕo Sùķà Jèfà Dan Bello A Mòta, Amma Sun Ce Kariya Sùkà Zo Ba Shi, Ba Wai Kama Shì Suķa Zo Yi Bà

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *