
Tsohon sakataren gwamnatin Najeriya, Babachir Lawal ya ce babban dalilin da ya sa ya bi haɗakar ƴan hamayya a ƙasar shi ne “rashin jin shawarwarin” da shi da kuma sauran ƴan Najeriya ke bai wa shugaban ƙasar Bola Tinubu.
Babachir na cikin ƴan siyasar Najeriya masu hamayya da suka fi jan hankali bayan ganin su cikin waɗanda suka ja tunga suka dunƙule domin samar da jam’iyyar da za ta ƙalubalanci shugaba Tinubu a zaɓen shekara ta 2027.
Ƴan adawar sun zargi gwamnatin Tinubu da gazawa wajen biyan buƙatun al’ummar ƙasar, duk da cewa wasu na ganin cewa ya yi wuri a yanke hukunci.
A tattaunawarsa da BBC tun bayan ayyana jam’iyyar ADC da ƴan hamayyar suka yi a matsayin lemarsu, Lawal ya zargi Tinubu da yanke hukunci kan manufofi masu gagarumin tasiri ba tare da shawartar masana ba.
“Janye tallafin mai (fetur) da ya yi bai yi tunani a kai ba, da zaman sa shugaban ƙasa cikin minti ɗaya ya janye tallafi, ba ya da minista, ba ya da kowa, shi kaɗai ya janye,” in ji Babachir.
Bola Tinubu ya janye tallafin man fetur ne a ranar 29 ga watan Mayun 2023 lokacin jawabin karɓar mulki a matsayin sabon shugaban Najeriya.
Ana kallon janye tallafin a matsayin ɗaya daga cikin manufofin shugaban ƙasar da suka haifar da tsadar rayuwa da tashin farashin kayan masarufi, wani abu da har yanzu al’ummar ƙasar ke kokawa a kai.
Sai dai Tinubu ya ce ya yi hakan ne domin rage kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa wajen biyan tallafin waɗanda za a iya amfani da su domin ayyukan ci gaban ƙasa, tare da cewa za a ga amfanin matakin a nan gaba.
Babachir Lawal ya shaida wa BBC cewa ba adawa yake yi da Tinubu ba, sai dai yana adawa ne da manufofin gwamnatin shugaban ƙasar, kuma a halin yanzu yana farin cikin rashin goyon bayan Tinubu tun farko.
“Ni adawata da nake yi shi ne a kan wasu ayyukan da yake yi (Tinubu) waɗanda ba su yi daidai ba, na yi sa’a da ban bi shi tun da farko ba, don abubuwan da Bola ke yi a yanzu, in da ina wurin, da ko dai an kore ni ko kuma na ajiye aiki saboda wahalar da manufofinsa suka kawo wa ƴan Najeriya,” in ji Babachir.
Babachir ya daɗe yana nuna adawa ga Tinubu tun kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2023 wanda ya bai wa Tinubu nasara.
A wancan lokacin Babachir ya nuna adawa da matakin jam’iyyar APC na amincewa da Kashim Shettima a matsayin mataimaki ga Bola Tinubu, kasancewar su mabiya addini ɗaya duk kuwa da cewa sun fito ne daga sassa daban-daban na ƙasar.
Ko bayan zaman Tinubu shugaban ƙasa, Babachir ya sha fitowa fili yana sukar sa tare da zargin shi da haifar da rarrabuwar kawuna.
A ƙarshen watan Yunin 2025 ne tsohon sakataren gwamnatin na Najeriya ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar.
A farkon watan Yuli ne manyan ƴan adawa a Najeriya suka bayyana jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a matsayin wadda za su yi amfani da ita domin ƙalubalantar Shugaban Tinubu a babban zaɓen Najeriya na 2027.
Hakan ya biyo bayan gaza kammala yi wa jam’iyyar ADA rajista daga hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasar, INEC.
Ƴan adawar da suka sanar da komawa jam’iyyar sun hada da ɗan takarar shugaban ƙasa na babbar jam’iyyar adawa a Najeriya (PDP) a zaɓen 2023, Atiku Abubakar da na jam’iyyar LP Peter Obi.
Haka nan akwai wasu manyan ƴan siyasa daga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da ta shuɗe, wadanda suka hada da ministoci da kuma muƙarrabansa.
Masana siyasa na kallon haɗewar ƴan adawar a matsayin wani yunƙuri na maimata abin da ya faru a shekarar 2013 lokacin da manyan jam’iyyun adawa uku na ƙasar suka haɗe wuri ɗaya suka samar da jam’iyyar APC (All Progressive Congress) wadda ta karɓe mulki a shekarar 2015.
Sai dai masu nazari na ganin cewa ya yi wuri a yi hasashen nasara ko rashin nasara da sabuwar haɗakar za ta samu, amma ɗaya daga cikin abubuwan da ake ganin za su zame mata matsala shi ne burin jiga-jigan da suka haɗa ta na zama ƴan takarar shugaban ƙasa.