Mataimakin shugaban ƙasar Malawi, Saulos Chilima ya mutu sakamakon haɗarin da jirgin da ke ɗauke da shi ya yi ranar Litinin.
Shugaban ƙasar ta Malawi, Lazarus Chikwera ya ce “jirgin nasa ya daki dutse” ne inda jirgin ya tarwatse kuma mista Chilima da dukkan waɗanda ke cikin jirgin suka rasu.
An dai samu tarkacen jirgin ne a kusa da wani tsauni.
An dai kwashe awanni ana bincike domin gano jirgin saman da ke ɗauke da mataimakin shugaban ƙasar Malawi.
Jirgin saman ya ɓace ne a ranar Litinin da safe.
Ana tunanin ya faɗi ne a dajin Chikangawa Forest da ke arewacin ƙasar.
Ya fuskanci rashin kyawun yanayi abin da ya sa aka hana jirgin sauka a filin jirgin sama na Mzuzu.
Shugaban Malawi ya ce ya ba da umarnin a ci gaba da aikin ceto mataimakinsa Saulos Chilima har sai an gano jirgin da ke ɗauke da shi da wasu mutane tara.
Shugaba Lazarus Chakwera ya ce babu shamaki da za a sanya wa aikin.
Ya ce yana cike da fatan gano mutanen da ransu.
Ana sa ran mataimakin shugaban kasar da ya ɓace zai yi takara da mai gidansa shugaba Chakwera a zaɓen shugaban ƙasar na shekara mai zuwa.
Wane ne Saulos Chilima?
Kafin shiga harkokin siyasa, Dr Chilima ya riƙe muƙamai a manyan kamfanoni kamar Unilever da kuma Coca Cola.
Shekarunsa 51. Yana da mata da ƴa ƴa biyu.
Shafin gwamnati ya bayyana Dr Chilima a matsayin “mai aiki tuƙuru” wanda “ba ya gajiya”.