
Rashin ganin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi a wajan jana’izar Buhari a Daura ya jawo cece-kuce sosai.
An yi ta yiwa Peter Obi Allah wadai da rashin halartar Jana’izar Buharin.
Daya daga cikin wadanda suka soki Peter Obi din akwai Tsohon Hadimin Goodluck Jonathan, Reno Omkri wanda yace masa ya manta da maganar samun kuri’un ‘yan Arewa.
Yace rashin halartar Peter Obi wajan jana’izar Buhari ya nuna irin kiyayyar da Peter Obi kewa yankin Arewa.