
.Rahotanni sun ce a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ‘yan Najeriya sun kashe jimullar dala Biliyan $29.29 wajan zuwa kasashen waje neman magani.
Hakan na nufin ‘yan Najeriya sun rika kashe akalla dala $3.6 duk shekara wajan neman magani a kasashen waje a shekaru 8 da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi yana mulki.
Hakan ya bayyana ne daga bayanan da babban bankin Najeriya, CBN ya fitar.
Hakan ya nuna irin yanda ‘yan Najeriya suka dogara da kasashen waje wajan neman magani.