DA ƊUMI-ƊUMI: Sowore Ya Maka Hukumar Ƴan Sandan Nijeriya A Kotu Kan Sace Masa Gilashi

Daga Muhammad Kwari Waziri
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa kuma ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin ɗan adam, Omoyele Sowore, ya shigar da ƙara a kotu yana zargin wani jami’in ‘yan sanda da sace masa gilashin AI mai ƙayatarwa yayin zanga-zangar da aka gudanar a hedikwatar rundunar ƴan sanda da ke Abuja.
A cewar Sowore, jami’in wanda aka bayyana sunansa da “Victor”, yana aiki ne a matsayin mai ɗaukar bidiyo na ƴan sanda a ƙarƙashin CSP Muyiwa Adejobi, ya sace gilashin ne da nufin su fitar da bayanan bidiyo da gilashin ke ɗauka.
Lauyan Sowore ya buƙaci a cafke jami’in tare da dawo da gilashin, yana mai cewa hakan ya nuna cin zarafi da amfani da iko ba bisa ƙa’ida ba.
Sowore ya bayyana cewa gilashin na da fasahar zamani da ke ɗaukar bidiyo da murya, kuma akwai muhimman bayanai da ke ciki dangane da yadda zanga-zangar ta gudana.
Ana ci gaba da sa ido kan yadda shari’ar za ta kaya.