Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya yi wa fursunoni 110 afuwa a wata ziyara da ya kai a babban gidan gyara hali da ke cikin garin Kaduna.
Gwamnan ya ɗauki matakin ne a ranar Talata, kwana ɗaya gabanin bukin ranar dimokuraɗiyyar ƙasar wanda zai gudana a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu.
Uba Sani wanda ya kuma bai wa fursunonin da aka yi wa afuwar naira 30,000 a matsayin kuɗin mota.