
Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar ADC, Nafi’u Bala wanda kuma dan takarar gwamna ne na jam’iyyar a jihar Gombe ya fito yayi ikirarin cewa shine ahugaban riko na jam’iyyar.
Ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya fitar da tsakar dare.
Yace ba zasu amince da David Mark a matsaykn shugaban jam’iyyar na riko ba inda yace an karya doka da aka baiwa wadanda ba asalin ‘yan jam’iyyar ragamar shugabancin jam’iyyar ba.
Hakan na zuwane bayan da aka mikawa David Mark shugabancin jam’iyyar na riko.